1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girka sabuwar rundunar kasashen yankin Liptako-Gourma

Salissou Boukari
January 25, 2017

Kasashen Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar, sun amince da girka wata runduna ta hadin gwiwa da za ta kula da harkokin tsaro a yankin Liptako-Gourma na kewayen iyakokin kasashen uku.

https://p.dw.com/p/2WLb1
Burkina Faso Präsidentengarde Soldaten
Sijojin kasar Burkina FasoHoto: Getty Images/AFP

A halin yanzu wannan yanki na iyakokin kasashen uku, ya zamana wata maboya ta 'yan ta'adda, kuma shuganannin da suka hada da Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar, da Roch Marc Christian Kaboré na Burkina Faso, da kuma Modibo Keïta Firaministan kasar Mali, dukanninsu sun amince da kafa wannan runduna ta sojoji, yayin wani babban zaman taron kungiyar ta kasashen uku da ya kammala da yammacin ranar Talata a birnin Yamai na Nijar.

Sanarwar karshen taron ta ce duk da kokarin da kasashe membobin wannan kungiyar ta Liptako-Gourma ke yi tare da tallafin manyan kasashe na duniya, har yanzu ana fuskantar matsalar tsaro a wannan yanki. Wannan mataki dai ya kasance irin wanda kasashen Nijar, Chadi, Kamarun da Nijeriya suka dauka a yankin tafkin Chadi a yakin da suke da 'yan kungiyar Boko Haram.