Gobara a masana'antar Gas a Saudi Arabia
November 18, 2007Talla
Akalla mutane 28 suka rasa rayukansu kawo yanzu,biyar daga cikin kuwa ma’aikatan kamfanin Saudi na Aramco,a wani haɗarin gobara data ɓarke a bututun iskar gas a yankin gabashin kasar Saudiyya da safiyar yau.Sanarwa daga kakakin kamfanin na nuni dacewar,ma’aikatan kamfanin ne suka yi sanadiyyar wannan wuta a cibiyar iskar gas din dake Hawiyah,alokacinda su ke haɗa sabbin wayoyi da yammacin jiya.Rahotanni na nuni dacewar a´yanzu dai an shawon kann gobarar,kuma wannan haɗari bazai shafi harkokin fitar da iskar gas din ba.