1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gomman 'yan mata sun bata bayan harin Boko Haram

February 21, 2018

Kimanin dalibai ‘yan mata 94 majiyoyi suka ce sun bace bayan da Boko Haram ta kai hari ranar Litinin da dare a wata makarantar mata da ke garin Dapchi a jihar Yobe.

https://p.dw.com/p/2t4j8
Boko Haram
Mayakan Boko Haram lokacin wani hari a bayaHoto: Java

Iyaye da dama sun shiga cikin rudani da damuwa saboda rashin sanin inda 'ya'yansu suka shiga kwanaki biyu bayan da kungiyar Boko Haram ta kai hari a makarantar sakandaren 'yan mata da ke garin Dapchi a karamar hukumar Burasari ta jihar Yobe.
Da yawa daga cikin daliban dai sun koma makaranta daga wuraren da suka gudu, sai dai akwai da dama da har yanzu ba a san inda suke ko halin da suke ciki ba.


Bayan da aka tattaro dalibai hukumar makarantar ta yi kiran suna daya bayan daya a gaban jami'an tsaro da jami'an gwamnati da wasu iyaye inda aka gano dalibai 94 daga cikin dalibai 1133 da ke makarantar ba su dawo ba.

Bakin motoci sun kai dauki


A'ishatu Abdullahi daya daga cikin dalibai da suka tsira daga harin ta ce lokacin da aka kai harin cikin dimuwa wasu daliban sun shiga wasu motoci da ba a san ko na wasu wane ne ba, ba a kuma san inda suka je ba.
Sai dai babu tabbacin ko 'yan kungiyar Boko Haram ne suka sace su yayin harin ko kuma sun bace a cikin daji ne yayin da suka yi gudun tsira da rayukansu.
Alhaji Kalwuri mai shago a Karasuwa mahaifin Maryam Kalwuri ne, daya daga cikin dalibai da har yanzu ba a ji duriyarsu ba.

"Mun mun tura mutane uku su je makarantar su tantance su a dawo da su. Da aka je sai aka ce an samu guda 15 daga cikin 16 da suka je karatu makarantar daga Karasuwa to daya da ba a samu ba, ita ce Maryam 'yata. Muna rokon Allah Ubangiji ya dawo mana da ita gida lafiya. Ko daji ta shiga ko kuma an tafi da su ne ko kuma me ya faru da ita Allah A'alamu"

Tantance yawan wadanda ba a gansu ba

Screenshot mutmaßliches Boko Haram Video
Daruruwan 'yan mata Boko Haram ta yi awon gaba da su lokacin da ta kai hari a makarantar 'yan mata ta Chibok a 2014Hoto: youtube/Fgghhfc Ffhjjj


Ya zuwa yanzu dai hukumomi ba su ce komai kan bacewar dalibai matan ba, sai dai tuni aka sanar da rufe makarantar na takaitaccen lokaci domin bai wa daliban damar komawa su gana da iyalansu kafin su dawo su ci gaba da karatu.
Alhaji Madu Aji Ajiri babban sakatare a ma'aikatar ilimi ta jihar Yobe ya tabbatar da rufe makarantar sai dai ya ce ana kan tantanace dalibai da suka dawo kafin a iya sanin yawan wadanda suka bata.

Yanzu haka iyaye da dama sun yi cirko-cirko a makarantar suna zaman jiran tsammani na dawowar 'ya 'yansu.

Masharhanta sun nemi hukumomi su gaggauata sanar da halin da ake ciki saboda gudun abin da ya faru lokacin da Boko Haram ta kwashe 'yan matan sakandaren Chibok a shekarar 2014.