1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gordon Brown ya ajje takara zama saban Praministan Britania

May 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuLf

Kwana ɗaya bayan alƙawarin da Praministan Britania, Tony Blair yayi, na sauka daga muƙamin sa, ranar 27 ga watan mai kamawa, ministan kuɗi na wannan ƙasa Gordon Brown ya bayyana ,shawar cenji Praministan mai barin gado.

Brown ya bayyana hakan, a wani taron manema labarai da ya kira yau, a birnin Londoon.

Ɗan takarar ya bayyana kyaukyawan burin da ya ke ɗauke da shi, na ƙara bunƙasa tattalin arzikin Britania.

Ko kamin Gordon Brown ya fito fili ya yi wannan bayyani, tuni al´ummar ƙasa na ɗaukar sa a matsayin mutumen da ya cencenji hawan wannan muƙami.

Shi kansa Praministan mai murabus, yayi masa cikkakar shaida.

A yayin da ya ke bayyani a game da mu´amila tsakamnin Britania da ƙasashen ƙetare, Gordon Brown yayi imanin cewar Engla ta tabka kura-kurai a game da yakin ƙasar Irak.