1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwar Hurricane na ci gaba da barazana

August 19, 2007
https://p.dw.com/p/BuDh

Mahaukaciyar guguwa da akewa lakabi da suna Hurricane Dean, tayi ajalin mutum na hudu a Dominican, a yayin da take ci gaba da nausawa izuwa Jamaica. A jiya sai da mahaukaciyyar guguwar tayi asarar rayuka uku, a tsibirin Santilushia da Matines, bayan barna mai yawan gaske da tayi. Masu nazarin yanayi na hasashen cewa , mahaukaciyar guguwar dake ratsawa ta yankin Caribiyan, ka iya kara karfi har ta kai mataki na 5, wanda kusan shine mafi hatsari. A cewar rahotanni, a yanzu haka guguwar na gudun kilomita 260 a cikin sa´a daya. Ana dai sa ran daga nan izuwa wani lokaci a yau, mahaukaciyar guguwar zata ratsa izuwa kasar Jamaica.Tuni dai al´ummar kasar suka kasance cikin shirin kota kwana. Haka suma al´umman kasashen Mexico da kudancin Amurka , tuni suka yi nisa na shirin kota kwanan jiran wannan mahaukaciyyar guguwa ta Hurricane Dean.