1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwar Irma ta isa gabar kogi a Florida

Abdullahi Tanko Bala
September 10, 2017

Dubban daruruwan mutane sun rasa wutar lantarki a Florida da ke Amirka sakamakon guguwar Irma tare da barazanar haddasa mummunan ta'adi.

https://p.dw.com/p/2jg7Y
Hurrikan Irma | USA, Florida | Miami
Hoto: Reuters/C. Barria

Guguwar Irma na kara yin karfi yayin da ta ke shirin yin dirar mikiya a Florida a yau Lahadi hade da ruwan sama kamar da bakin kwarya da kuma barazanar ta'adi mai yawa wanda ya tilasta kwashe jama'a daga gidajen su a wani lamari mafi girma da ba'a taba gani ba a tarihin kasar Amirka.

Mahaukaciyar guguwar wadda ta fara yin mummunan barna a yankunan gabar kogi a Kuba tana tafiyar kilomita 210 cikin sa'a guda a kudu maso gabashin Florida a cewar cibiyar nazarin guguwa ta kasar.

Guguwar ta Irma wadda hallaka akalla mutane 22 a yankin Caribbean, an yi kiyasin za ta haddasa ta'adi na biliyoyin daloli.

A halin da ake ciki an sami katsewar wutar lantarki a gidaje kusan dubu 500 a Florida sakamakon guguwar.