1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwar Wilma ta doshi jihar Florida

October 24, 2005
https://p.dw.com/p/BvO8

Mahaukaciyar guguwar Wilma na ci gaba da hadasa assarorin rayuka, da na dukiyoyi, a wurarren da ta ke ratsawa.

Bayan gabar tekun Mexico, inda ta hadasa mutuwar mutane 8 a daren jiya,da kuma Kuba, inda ta jawo barna mai tarin yawa,Wilma a halin da ake ciki, ta doshi jihar Florida a kasar Amurika.

Hukumomin jihar sun yi kira ga al´ummomin da su ka ki barin gidajen su, don kauracewa guguwa, da su kasance a wuraran buya masu tabbas , sannan a daya hannun, kar su yi kwankwanto da tabbatacen tallafi, daga gwamnati, domin su da kansu su ne, su ka tarbi aradu da fadin rai

Da dama daga mazamna yankin keys da ke kudancin Florida sun bayana kosawa, da guje-gujen hijira,a duk da lokacin da a ka samu matsalar guguwa.

Sun bukaci zama a gidajen su, su rungumi kaddara.

Gwamnan jihar Florida Jeb Bush ,ya nuna matukar rashin gamsuwa da halayen taurin kai,da wannan al´ummomin su ka nuna.

A halin da ke ciki jami´an agaji na jihar Florida, sun yi jiggilar dubunnan mutane daga gidajen su, a shirye shiryen issowar wannan saban bala´in guguwa, bayan na Katrina da Rita.