1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guido Westerwelle yana fatan samun zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya

May 24, 2010

A yau litinin itama shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta fara ziyara a yankin gabas ta tsakiya

https://p.dw.com/p/NVY8
Shugaban Masar Hosni Mubarak na ganawa da Ministan harkokin wajen Jamus Guido WesterwelleHoto: AP

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle yayi kira ga shugabannin yankin gabas ta tsakiya dasu bada tasu gudumawar wajen kawo zaman lafiya a yankin.

A ƙarshen ziyarar daya kai yankin, Westerwelle ya gana da Sarki Abdallah na biyu na Jordan da shugaban Syriya Bashar al-Assad da nufin ganin sun taimaka wajen shirya ganawa ta ƙeƙe da ƙeƙe tsakanin Israilawa da kuma Palasɗinawa.

A lokacin ganawar tasu ministan harkokin wajen na Jamus yayi kira musanman ga Syriya data nisanta kanta daga ƙungiyoyi masu tsattsuran ra'ayi da basa ƙaunaran ganin anyi wannan ganawar.

Tunda farko dai saida Westerwelle ya gana da shugaban Masar Husni Mubarak a ranar Asabar bayan ya ziyaraci Lebanon. A yau litinin itama shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel zata fara ziyara a yankin gabas ta tsakiya.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Yahouza Sadissou Madobi