1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guinea ta sassauta dokar hana fita da ta kafa bayan rigingimu a kasar

February 19, 2007
https://p.dw.com/p/BuRT

Gwamnatin kasar Gini ta dan sassauta dokar hana fita da ta kafa bayan an samu raguwar zanga-zangar nuna kyamar mulkin shekaru 23 na shugaba Lansana Conte. Wata sanarwa da hafsan hafsoshin soji Janar Kerfala Camara ya bayar ta yi nuna da cewa tun daga yau litinin ´yan kasar ka iya fita daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma. A ranar litinin ta makon jiya aka kafa dokar tabaci a kasar dake yammacin Afirka don dakile jerin zanga-zanga da wani yajin aiki na gama gari da wanda sakamakon sa akalla mutane 100 suka rasu. Shugabannin kungiyoyin kwadago na neman shugaba Conte yayi murabus.´Yan adawa sun ce an kame mutane kimanin 100 tun bayan kafa dokar tabacin.