1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Uwargidan Laurent Gbagbo za ta gurfana a gaban kuliya

Kamaluddeen SaniMarch 18, 2016

Lauyan da ke kare uwargidan tsohon shugaban kasar Cote d'ivoire Simone Gbagbo ya sanar da cewa za ta gurfana a gaban kuliya a ranar 25 ga watan Afrilu mai zuwa.

https://p.dw.com/p/1IFqt
Elfenbeinküste Simone Gbagbo
Hoto: picture-alliance/AP Photo/R. Blackwell

Simone Laurent Gbagbo da ake mata lakabi da Iron Lady mai shekaru 66, tuni aka yanke mata hukuncin zaman gidan yari a shekarar da ta gabata kan irin rawar da ta taka a dangane da rikicin bayan zaben kasar da ita da mai gidanta a shekara ta 2010. Kotun Kasa da Kasa da ke Hukunta masu Aikata Manyan Laifuka wato ICC da ke da zama a birnin The Haque na kasar Neatherlands ma dai ta bada sammacin kamo Simon Gbagbo, koda yake kawo yanzu gwamnatin ba ta mika ta ba. Duk dai da matsin lambar da kotun ta ICC ta yi na a mika ta, shugaban kasar ta Cote d'ivoire Alassane Ouattara ya yi kememe a inda ya ce bangaren shari'ar kasar ma zai iya yanke mata hukunci cikin adalci.