1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

290810 Guttenberg Afghanistan

August 30, 2010

Ministar tsaron Jamus, Karl -Theodore zu Guttenberg a karon farko ya gana da sojojin Jamus a Afghanistan

https://p.dw.com/p/OzVW
Ministan tsaron Jamus Karl-Theodor zu Guttenberg,Hoto: AP

Wannan dai ba shine karon farko da Ministar tsaron na Jamus, Karl-Theodor Zu Guttenberg ya kai ziyara zuwa Afghanistan ba, sai dai wannan ne karon farko da ya yi ido huɗu da sojojin a filin daga. Guttenberg  ya sauka ne a jirgi mai saukar Ungulu a ɗaya daga cikin tashoshin sojojin, wanda ke tazarar Kilometer 15 daga wurin da sojojin Jamus guda huɗu suka rasa rayukan su a harin kwantar ɓaunar da yan Taliban suka yi musu. Sojojin suna aikin sintiri ne a yankin arewacin Baghlan tare da haɗin gwiwa da sojojin Afghanistan. A lokacin da yake ganawa da sojojin Ministan ya yi musu jawabi yana mai cewa " Ina da muhimmanci a gare ni na ga yadda halin da dakarun sojin mu ke ciki bama kaɗai a gida ba, har ma a sansanoninsu a filin daga dake Afghanistan. Babban maƙasudi shine domin ƙarfafa muku gwiwa sannan na fahimci halin da kuke ciki da irin ƙalubalen da ku ke fuskanta. Ta hakan ne kuma zan sanar da jama'ar mu a gida gagarumin aikin da ku ke gudanarwa wanda ku ka shafe tsawon makonni goma sha ɗaya kuna yi cikin mawuyacin yanayi.

Wannan dai ita ce ziyararsa ta biyar a Afghanistan tun bayan da ya fara aiki a watan Oktoban bara. Guttenberg ya yi ƙoƙarin tsayawa domin ziyartar sojojin a watan Yuli amma bai samu yi hakan ba saboda harin da ƙungiyar Taliban ke kaiwa a daidai wannan lokacin.

Lammert / Guttenberg / Afghanistan / Ehrenhain
Wasu daga cikin sojojin Jamus a Afghanistan tare da Ministan tsaro Karl Theodor Zu- GuttenbergHoto: AP

Guttenberg yayi wannan ziyarar ce tare da kakakin majalisar dokokin Jamus, Nobert Lammert, bayan da suka ziyarci sojojin, Lammert ya ƙarasa zuwa Kabul domin ya gana da shugaban ƙasar Afghanistan Hamid Karsai da kwamandan rundunar sojojin Amurka a Afghanistan, General David Patraeus.

" Yace abin farin ciki ne cewa fasalin dabarun da ake gudanarwa suna yin nasara. Wannan shine burin mu kuma abin da nake fatan gani kenan. Za mu yi bakin kokari wajen fahimtar da jama'ar mu a gida  wannan gagarumin aiki da kuke yi.

Muƙarraban Karzai sun gayawa Lammert cewa Kabul tana son Jamus ta taka rawar gani sosai wajen aiko da ƙarin sojoji domin Majalisar Jamus tana da ƙarfin faɗa a ji wajen aikewa da sojoji zuwa ƙasashen waje. Ko da yake Guttenberg ya ƙara bayyanawa sojojin cewa a yanzu haka dai ƙasar tana da dakaru 250,000 daga sassa na rundunar sojojin a saboda haka yace sojoji 7000 ne kaɗai Jamus za ta iya turawa.

Mawallafa : Kai Küstner / Pinado Abdu

Edita : Abdullahi Tanko Bala