1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwagwarmaya yanzu aka fara inji Mr Haniyya

December 8, 2006
https://p.dw.com/p/BuYm

Faraministan Yankin Palasdinawa, Isma´il Haniyya yace, gwamnatin da Kungiyyar Hamas take jagoranci a yankin, ba zata taba amincewa da kasancewar kasar Israela ba.

Isma´il Haniyya , ya fadi hakan ne kuwa yayin da yakewa dubbannin daliban jami´ar birnin Tehran jawabi, a lokacin sallar juma´a, a yau.

Faraministan na Palasdinawa, dake ci gaba da ziyarar sa ta aiki a kasar ta Iran, yaci gaba da cewa Palasdinawa zasu ci gaba da gwagwarmaya har lokacin da zasu yantar da yankin su izuwa kasa mai cin gashin kanta.

Wannan mataki dai da gwamnatin ta Hamas ta dage a kansa na daga cikin dalilan daya haifar kasar Amurka da kungiyyar Eu dakatar da irin tallafin raya kasa da suke bawa yankin.

Daga dai tun lokacin da kasashen yamman suka dauki wannan mataki, kasar Iran ta dauki matakin rubanya irin tallafin raya kasa da take bawa yankin na Palasdinawa.