1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwagwarmayar gina sabon masallaci a birnin Straßburg

YAHAYA AHMEDOctober 25, 2006

A ran 1 ga watan Satumba ne aka fid da harsashen ginin babban masallacin birnin Straßburg a ƙasar Faransa. Ana dai kyautata zaton cewa, idan an gama gina shi, masallacin zai iya kasancewa gun ibada ga musulmi kusan dubu ɗari 8 da ke zaune a jihar Alsace ta Faransan, wadda Straßburg din ce babban birninta.

https://p.dw.com/p/BvTD
Ginin majalisar mashawartan Tarayyar Turai a birnin Straßburg
Ginin majalisar mashawartan Tarayyar Turai a birnin StraßburgHoto: picture-alliance/ dpa

A ɓangaren ɗaya dai, a huskar siyasa, ana ganin gina masallacin ne tamkar wata alama da ke nuna karɓuwar da addinin islama ya samu a nahiyar Turai, saboda birnin Straßburg ɗin ne kuma mazaunin Majalisar Mashawarta ta tarayyar Turan da kuma Majalisar Ƙungiyar Haɗin Kan Turai. Amma a ɗaya ɓangaren kuma, ana ta ƙara samun ’yan ƙasar Faransan, musamman mazauna wannan jihar ta Alsace, masu daddage wa shirin gina masallacin. A jihar dai, an ƙiyasci cewa kashi 30 cikin ɗari na al’umman ne ke ka da wa jam’iyyar nan Front Nattional ƙuri’u. Ita dai wannan jam’iyyar sananniya ce wajen bin tsatsaurar ra’ayi da kuma nuna matuƙar ƙyama ga baƙi. Saboda daddage wa shirin gina masallacin da masu adawa da shi suka yi ta yi ne, aka rage girmansa da kuma tsawon hasumiyoyinsa.

Daidaiton da aka cim ma kafin a sami aminccewar hukumar birnin ta ba da izinin gina masallacin, ya ƙunshi wasu sharuɗɗa ne, waɗanda suka haɗa da rage girman kubban masalllacin da hasumiyarsa. Bugu da ƙari kuma, ba za a faɗaɗa ginin da wata cibiyar al’adu ba. Duk da hakan dai, musulman birnin na Straßburg sun ce sun cim ma burinsu na ganin cewa an gina masalllacin. Kuma za su iya tafiyad da harkokin addininsu, duk da cewa ba kamar yadda suka tanadi yi da farkko ba. Limamin masallacin birnin da ake amfani da shi yanzu, Abdelhamid Youyou, ya bayyana cewa:-

„Da farko kam sai da muka huskanci matsaloli, wannan zan iya tabbatar maka da haka. Burinmu ne mu giina masallacinmu a cikin wannan birnin, wanda ake kambama shi tamkar cibiyar tarayyar Turai. Muna son kuma masallacinmu ya cancanci matsayin birnin Straßburg, wanda shi ne mazaunin Majalisun tarayyar Turai da ƙungiyar Haɗin Kan Turai. Ta yin la’akari da haka, kamata ya yi girman ginin masallacinmu ma ya nuna wannan matsayin.“

Tun shekaru 25 da suka wuce ne dai Imam Abdelhamid Youyou ke jagorancin musulmin birnin wajen ibada, a cikin wani zauren da aka mai da shi masallaci, bayan wani babban gini. Gun ibadan dai ya ƙanƙanta ga ƙarin yawan muslmin da ake samu a birnin. Sabili da haka ne dai ƙungiyar musulmin birnin na Straßburg ta miƙa bukatunta na samun izinin gina babban masallaci ga mahukuntan birnin. To sai dai, shugabannin hukumar birnin, masu bin ra’ayin mazan jiya, ba su ga wani muhimmancin da gina wannan gagarumin masallacin ke da shi ba. Saboda a nasu ganin, har ila yau addinin islama wata baƙuwar al’ada ce a yankin.

Ga ’yan siyasa da mazaunan birnin Straßburg ɗin dai, gina masallaci mai kubba, da hasumiya, da kuma kiran sallah da ake yi da lasifika tsakanin gine-ginensu na gargajiya da ke yankin tsohon garin birnin, ba abin da za su iya amincewa da shi ba ne.

Bayan dai jayayyar da ƙungiyar musulmin ta shafe shekaru da dama tana yi da mahukuntan birnin, sai aka cim ma daidaito, inda hukumar birnin ta ba da filin gina masallacin kyauta. Sai dai da akwai wasu sharuɗɗa da aka gindaya wa ƙungiyar musulmin, na cewa masalllacin ba zai kasance yana da hasumiya ba. Kuma, ba za a yi amfani da tallafi daga ƙetare wajen gina masallacin, wanda zai ci kuɗi kimanin Euro miliyan 4 da rabi ba. Mahhukuntan birnin dai na fargabar cewa ’yan tsagerun islama za su iya mamaye masallacin su mai da shi sansanninsu, idan aka amince da samo taimako daga ƙetare.

Fida da harsashen ginin da aka yi a farkon watan Satumban da ya gabata dai, na alamta kawo ƙarshen ka ce na ce da aka yi ta yi ne tsakanin Hukumar birnin da ƙungiyar islaman, inji Imam Abdelhamid Youyou, wanda kuma yake ƙoƙarin kyautata hulɗa tsakanin ɓangarorin biyu don a manta da rashin jituwar da aka samu:-

„Na yi imanin cewa, mafi yawan jama’a a nan jihar Alsace sun amince da shirin gina masallacin. Sun san dai cewa, wannan shirin zai janyo fa’ida ga dukkanmu. A zamanin nan da muke ciki dai, muna zaman duniya ne na cuɗe-ni, in cuɗe-ka, inda duk al’adu ke hulɗa da juna, duk da bambancinsu. Ko’ina dai na sha jin ana yayata haka, ko a rediyo ne da talabijin da dai sauransu.“

A kan titunan birnin kam, ba a jin wannan labarin na tuntuɓar juna da al’adun ke yi. Wannan jihar ta Alsace dai, ta fi ko wacce a Faransa magoya bayan jam’iyyar nan ta Front National, mai bin tsatsaurar ra’ayi, kuma mai matuƙar ƙyamar baƙi. A lokacin zaɓe, alƙaluma na nuna cewa, kashi 30 cikin ɗari na masu ka da ƙuri’u ne ke zaɓan wannan jam’iyyar. Kuma ba abin mamaki ba ne, ka ga a bayyane ma, ana amfani da wasu kalmomi na nuna ƙyama ga baƙi. Kamar dai yadda wani mutumin da ya bukaci kada a ambaci sunansa ya bayyanar:-

„Kai, waɗannan musulman da ke ta yaɗuwa a nan Faransa. Ba sa son cuɗanya da sauran jama’a. Cin moriyar tallafin da hukuma ke bai wa jama’armu kawai suke yi. Bayan haka, sai su yi ta cin karensu babu babbaka. Mu ne yanzu muke ƙasƙantad da kanmu gaban musulmin, amma duk da haka ƙyamar al’ummanmu suke yi.“

Shi dai wannan mutumin ya ce yana matuƙar ƙyamar ganin an gina wannan masallacin. Ba ya son kuma duk wani abin da zai haɗa shi da musulmi. Kai, a nasa ganin dai, duk wani abin da ba shi da asali daga jihar ta Alsace ma, kamata ya yi a kau da shi daga jihar gaba ɗaya

Shi dai Imam Abdelhamid Youyou da sauran musulmin birnin sun sha fama da irin waɗannan mutanen. Amma kamar yadda ya bayyanar, waɗannan mutanen ’yan tsiraru ne da ke son ta da zaune tsaye. Ko ta wace hanya ne za a iya shawo kan wannan matsalar? A ganin Imam Abdelhamid dai, idan an gama gina masallacin, za a iya buɗe shi ga duk masu sha’awa, su zo su gano wa idanunsu cewa, ba wani abin sirri ake yi ciki ba:-

„Burin wannan masallacin ne, ban da bai wa masu imani gun ibada, ya kasance kuma cibiyar tattauna batutuwan zaman lafiya da tuntuɓar juna, a duk lokacin da aka sami hauhawar tsamari. Hakan dai zai iya taimakawa wajen sulhunta rikice-rikice tsakanin al’umman da ke zanune a nan.“