1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnati a Nigeria zata tattaunawa da kwamamdojin sojin kasar

October 5, 2006
https://p.dw.com/p/BuhO

Mahukuntan Nigeria sun umarci manyan kwamandojin Sojin kasar dasu hallara a babban birnin tarayya , wato Abuja, domin tattaunawar gaggawa dasu.

Daukar wannan mataki dai daga bangaren mahukuntan na Nigeria, ya biyo bayan yadda rikici ke kara kazanta ne , a yankin Niger Delta Mai arzikin Mai ne.

Rahotanni dai sun rawaito yan kungiyyar mayakan sa kann nan ta Mend a jiya na cewa, sun sami galabar kashe sojin na Nigeria 17, to amma ya zuwa yanzu rundunar sojin kasar bata ce komai ba tukuna.

Bayan dai sako ma´aikatan man kamfannin Shell din nan 25, a yanzu haka ma´aikatan man ExoMobel su 7 na ci gaba da kasancewa a hannun tsagerun yankin na Niger Delta.

Bayanai dai sun nunar da cewa tsagerun yankin sun yi awon gaba da ma´aikatan man 7 ne a jihar Akwa-Ibom dake yankin na Niger Delta a jiya laraba.

Game da hakan kuwa, kakakin rundunar yan sandan Jihar ASP Shapa Zu ya tabbatar da cewa rundunar su na laluben tsagerun don cafke su tare da kubutar da yan kasashen ketaren.