1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnati mai ci ta lashe zaben kasar Kwango

Salissou BoukariMarch 24, 2016

A tsakiyar dare ne dai ministan cikin gida kasar Kwago ya sanar da sakamakon zaben shugaban kasar wanda Denis Sassou Nguesso ya lashe.

https://p.dw.com/p/1IIZf
Kongo Verfassungsreferendum - Präsident Denis Sassou Nguessou
Shugaba Denis Sassou NguessoHoto: Getty Images/AFP

Shugaban kasar Kwango Brazzaville Denis Sassou Nguesso wanda ya shafe fiye da shekaru 32 a kan karagar mulkin kasar, ya sake lashe zaben shugaban kasar da ya gudana na ranar Lahadin da ta gabata. Ya dai samu kashi 60 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada a cewar ministan cikin gidan kasar Raymond Zephyrin Mboulou.

Da wajejan karfe uku da rabi na dare ne dai ministan cikin gidan kasar ta Kwango ya sanar da wannan sakamako. A ranar Laraba dai biyu daga cikin 'yan takaran sun yi watsi da sakamakon da hukumar zaben kasar ta bayyana, da ya yi nuni da cewa shugaban kasar ne ke kan gaba da kashi 67 cikin 100. Tun farko dai gamayyar 'yan adawan na Kwango sun nuna rishin amincewarsu ga hukumar zaben kasar, inda suka kafa tasu ta kansu, abun da ya janyo kaste layukan sadarwa a kasar.