1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnati ta tsawaita dokar ta baci a Nijar

Salissou Boukari
September 16, 2017

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sake tsawaita dokar ta baci a yankin jihar Diffa da ke gabashin kasar da kuma yankin yammacin kasar inda nan ma ake fama da matsalar mayakan jihadi daga Mali.

https://p.dw.com/p/2k6be
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Shugaban kasar Nijar Issoufou MahamdouHoto: F. Batiche/AFP/Getty Images

Sanarwar gwamnatin ta Nijar ta ce, an kara tsawaita dokar ta bacin ne da watanni uku wadda kuma za ta soma daga ranar Litinin 18 ga wannan wata na Satumba a yankin jihar Diffa mai makwabtaka da Jihar Borno a Tarayyar Najeriya ganin yadda har yanzu harkokin tsaro suke da rauni. Sanarwar ta kara da cewa, a yankin yammacin kasar ma an kara tsawaita dokar ta bacin ta tsawon watanni uku, ganin yadda ake ci gaba da samun barazanar 'yan ta'adda da ke fitowa daga kasar Mali.