1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin ƙasar Côte d’Ivoire ta yi murabus.

September 7, 2006
https://p.dw.com/p/BukW

Rahotannin da ke iso mana daga birnin Abidjjan sun ce gwamnatin ƙasar Côte d’Ivoire ta yi murabus game da taɓargazar dagwalar masana’antun nan da aka jibge a ƙasar. Wasu majiyoyin gwamnatin sun ce Firamiyan riƙon ƙwarya Charles Konan Banny ya miƙa murabus ɗin majalisar ministocinsa ga shugaba Laurent Gbagbo, a wani taron gaggawar da suka yi a babban birnin ƙasar Yamoussoukro. Rahotanni dai sun ce shugaba Gbagbon ya amince da murabus ɗin.

Gabannin hakan dai, dubannin mutane sun yi zanga-zanga a kan titunan birnin Abidjan, bayan mutuwar wasu yara biyu da suka shaƙi hayaƙi mai guba daga dagwalar masana’antun da aka jibge a kewayen birnin. Rahotanni dai sun ce a ƙalla mutane kimanin dubu da ɗari 5 ne suka yi rashin lafiya sakamakon cuɗanyarsu da gubar. Jami’an ƙasar, sun ce an sauke dattin masana’antun ne a tashar jirgin ruwan Abidjan a watan jiya, daga wani jirgin ruwan da aka yi rajistarsa a ƙasar Panama, kafin a zub da su a wurare 8 a kewayen birnin.