1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Afghanistan na bukatar makudan kudade don sake gina kasar.

Mohammad Nasiru AwalMarch 31, 2004
https://p.dw.com/p/Bvkw
Shugaban Afghanistan Hamid Karzai da ministar raya kasashe masu tasowa ta Jamus Heidemarie Wieckzorek-Zeul
Shugaban Afghanistan Hamid Karzai da ministar raya kasashe masu tasowa ta Jamus Heidemarie Wieckzorek-ZeulHoto: AP

Tun bayan hambarad da gwamnatin Taliban da kawarta wato Al-Qaida ya fito fili cewar gamaiyar kasa da kasa zata fara taimakawa aikin sake gina Afghanistan. Kasar ta shiga cikin mawuyacin hali na tabarbarewar tattalin arziki sakamakon yake-yaken basasa da ta shafe shekaru 10 tana fama da su. Kasar dai ba zata iya samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma wadata ba, sai tare da taimakon kasashen duniya. A ma halin da ake ciki ana fargabar cewa kasar ka iya sake zama wani sansanin ´yan ta´adda.

Tun da farkon fari aka san cewar gwamnatin wucin gadi ta Afghanistan ba zata iya magance matsalolin wannan kasa ba, musamman wajen sake farfado da hanyoyin sadarwa da kwance damarun mayaka da kuma sake tsugunar da miliyoyin ´yan gudun hijira a kasar. Saboda haka kasashen duniya suka gudanar da wani taron a birnin Tokyo a cikin shekara ta 2002, da nufin tara makudan kudaden da ake bukata cikin gaggawa don sake gina Afghanistan. A karshen wannan taro wakilai daga kasashe kimanin 60 da kungiyoyin sa kai kusan 20 sun yi alkawarin ba Afghanistan taimakon kudi dala miliyan dubu 4.5. To amma har halin da ake ciki wani dan tamani aka ba ta.

Shi ma taron kasashen da suke tallafawa Afghanistan a birnin Berlin na tattaunawa ne game da batun samarwa kasar taimakon kudi. Saboda haka gwamnatin Afghanistan na halartar wannan taro ne tare da sanya dogon burin samun isassun kudaden taimako. A cikin wata hira da tashar DW ta yi da shi, ministan kula da ayyukan sake gina Afghanistan Mohammad Amin Farhang ya kiyasta cewar kasar sa na bukatar taimako na dala miliyan dubu 10 don tafiyar da ayyukan raya kasa a cikin shekaru 5 masu zuwa, wato dala miliyan dubu biyu a shekara. To amma alkalumman baya-bayannan sun yi nuni da cewa ana bukatar dala miliyan dubu 4 a duk shekara don sake gina Afghanistan. Wato kenan ana samun gibin dala miliyan dubu 2 a cikin kudin taimako da gwamnatin Afghanistan ke bukata daga gamaiyar kasa da kasa. Gwamnatin Afghanistan ta ce tana bukatar karin taimako don farfado da muhimman hanyoyin sadarwa da nufin kyautata halin rayuwar jama´a. Wani muhimmin abu da ake bukata shine sahihan matakai game da sake tsugunar da miliyoyin ´yan gudun hijirar kasa daga Pakistan da Iran. Idan aka yi la´akari da jan aikin da ke gabanta, za´a ga cewa ba abin mamaki ba ne da gwamnatin Afghanistan ke kara mika kokon bararta ga gamaiyar kasa da kasa don samun ko da kashi 60 cikin 100 ne na kudaden da take bukata don sake gina kasar.