1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Bush a Amirka ta fada cikin wani mawuyacin hali

October 29, 2005
https://p.dw.com/p/BvNV

Babban hafsan mataimakin shugaban Amirka Dick Cheney wato Lewis Libby zai gurfana gaban shari´a a dangane da wani abin kunya da ya shafia bayyana asalin wata jami´ar hukumar leken asirin Amirka CIA. Babban mai shigar da kara Patrick Fitzgerald ya nunar da haka a wani taron manema labarai a birnin Washington. Idan aka same shi da aikata wannan laifi Libby ka iya fuskantar dauri har na shekaru 30 a kurkuku tare da tarar kudi na sama da dala miliyan daya. ´Yan mintoci kalilan bayan tuhumarsa, Libby ya yi murabus. To sai dai ya sha nanata cewa bai aikata wani laifi ba. Ana kuma gudanar da bincike a kan Karl Rove babban mai bawa shugaban Amirka GWB shawara, ko da yake kawo yanzu ba´a tuhume shi ba. Tuhumar da aka yiwa Libby ta samo asali ne shekaru biyu da suka wuce na wani bincike akan ko da gangan jami´an fadar White House suka bayyana asalin jami´ar hukumar CIA, Valerie Plame ko kuma sun yi karya ne a gaban masu bincike. An dai bayyana asalinta ne ga kafofin yada labaru bayan da mijinta wanda dan diplomasiya ne, ya zargi gwamnatin Bush da kaddamar da wani haramtaccen yaki akan Iraqi.