1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Erdorgan ta samu nasarar amincewa da gyaran tsarin mulki

September 12, 2010

Kashi 58 na yawan Al'ummar Turkiyya sun amince da gyaran tsarin mulkin ƙasar

https://p.dw.com/p/PARQ
Hoto: AP

Ƙuri'ar raba gardama dangane da Gyaran fuskar kundun tsarin mulkin data tanadi rage karfin faɗa a ji da sojoji ke da shi a harkokin mulki a Turkiyya ya samu amincewa. Gidan talabijin na NTV mai zaman kansa a Turkiyyan ya ruwaito cewar kashi 58 daga cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa ne suka amince, zaɓen da kashi 75 daga cikin al'ummar Turkiyyan suka fito. Gwamnatin Priminista Recep Tayyip Erdogan ce ta bukaci a yi ƙuri'ar raba gardamar domin gyaran kundun tsarin mulkin, wanda ke da nufin sake tsarin sashin shari'a tare da rage ƙarfin ikon sojoji. Ɓangarorin biyu dai na fuskantar saɓani da gwamnatin Erdorgan mai ci a yanzu. Turkiyyan dai ta hakikance cewar waɗannan gyare gyaren ne zasu share wa ƙasar hanyar shiga ƙungiyar Tarayyar Turai, EU. Sai dai kusan dukkan jami'iyyun adawa ne suka bukaci masu kaɗa kuri'un su nuna adawa. Jami'iyar adawa ta kurdawa ta kauracewa zaɓen, domin a cewarta ba zai sauya komai a 'yancin su tsiraru ba.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita           : Abdullahi Tanko Bala