1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Eritrea ta hana jiragen Majalisar Dinkin Dunia shawagi a sararin samaniyar kasar ta

Yahouza SadissouOctober 6, 2005

Gwamnatin Eritrea ta hana jiragen majalisar dinkin dunia shawagi a sararin samaniyar kasar ta.Komitin Sulhu ya nuna bakin ciki

https://p.dw.com/p/BvZ8

Gwamnati Eritrea ta hana jiragen samar Majalisar Dinkin Dunia shawagi a sararin samaniyar kasar.

Komitin kwantar da tarzoma na Majalisar Dinkin dunia, na da jiragen sama masu saukar angullu da dama, a kasashen Eritrea da Habasha, wanda ke yin dimomi , ga sojojin shiga tsakani dake wannan kasashe.

Bayana wannan mataki ke da wuya, komitin sulhu ya shirya taron gaggawa, inda a baki daya, yayi tur da Allah wadai da wannan aniya da gwamnatin Erytrea ta dauka, wadda babu shaka zata haifar da koma baya, ga yunkurin cimma zaman lahia a wannan kasa.

A daya hanunn kuma, komitin sulhu ya danganta matakin da cin zarafi Majalisar Dinkin Dunia.

A game da haka sanarwar da komitin ya fido, ta yi kira ga hukumomin Asmara da su yi watsi da wannan kuduri, da ya sabawa doka mai lamba 1312, da ta girka rundunar kwantar da tarzoma ta Minuee, a kasashen Eritrea da Habasha, tun shekara ta 2000.

Mataimakin Sakatare Jannar, na Majalisar Dinkin Dunia Jean marie Gueheno, ya gargadi hukumomin Eritera, da na Habasha da su guji duk wasu take take, da kan iya sake tsunduma su cikin wani saban bila´in yaki.

Kuma ya zama wajibi inji shi, Eritera ta lahse amen ta, a kan wannan doka da ta dauka.

Sannan ya gayaci hukumomin kasashen 2 da su yi aiki sau da kafa da yarjejeniyar da su ka cimma ta shata iyakoki tsakanin su .

Habasha da Eritrera, sun yaki juna daga 1998, zuwa 2000, shekara da su ka rataba hannu a kan yarjejeniyar zaman lahia a kasar Algeria.

A sakamakon wannan yarjejeniya, bangarorin 2, sun amince da iyakar da komitin Majalisar Dinkin Dunia ya shata tsakanin su.

To saidai, jim kadan bayan yarjejeniyar bangarorin 2 su ka yi watsi da ita.

A game da haramcin tashin jiragen saman, na Majalisar Dinkin Dunia,har ya zuwa yanzu hukumomin Eritera ba su bada dallilan da su ka sa su, daukar matasyain ba, to saidai masharahanta na hasashen cewa, ba zai rasa nasaba ba da yawan shigi da ficin, da jiragen ke yi, a kasar ta Eritera.

Kakakin Majalisar Dinkin Dunia a Eritera, ya sanar manema labarai cewa, ba su da yancin bada umurnin tashin jiragen muddun ba su samu hadin kai ba,daga gwamnatin Eritera.

A game da haka, ya kara jaddada kira a ga gwamantin, da ta janye wannan kuduri.

Mudun kuma ta yi tsaye kan bakan ta, to babu makawa, cilas rundunar tsaron ta gama yanata yanata, ta fuce daga kasar, abinda kuwa zai hadasa barkewar saban yaki.