1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

290910 Frankreich Ausländerrecht

September 29, 2010

Jam´iyun adawa da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun yi Allah wadai da sabuwar dokar baƙi da gwamnatin Faransa ta gabatar gaban Majalisa

https://p.dw.com/p/PPv0
Majalisar Dokokin FaransaHoto: AP

Bayan rikicin ta aka tafka game da korar ´yan ƙabilar Roma da gwamnatin Faransa ta yi, yanzu kuma an shiga saban cece-kuce, game da  wata  doka da Majalisar Dokoki ta yi mahaura a kai jiya.

wannan doka ta tanadi ƙwace takardar zama cikkaken ɗan ƙasar Faransa ga duk bafaranshe baƙo, da ya aikata lefin dukar jami´in tsaro.

Ministan da ke kula da harakokin baƙi ne Eric Besson, ya gabatar da wannan ayar doka bisa umurnin shugaba Nikola Sarakozy.Babban burin wannan doka inji ministan shine ƙara kariya ga jami´an tsaro wanda a lokata da dama su kan shiga mungun hali a yayin zanga-zanga, mussamman a unguwanin baƙi ´yan ci rani.

Da dama daga faransawa tsatsanan baƙi na tamaƙa da takardun su na zama cikkakun ´yan ƙasa domin nuna ɓatanci ga jami´an tsaro.

To saidai wannan doka ta ci karo da turjiyar jam´iyun adawa da kuma Ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bani adama.

Armelle Gardien jami´a ce a Ƙungiyar kare haƙƙin ´yan gudun hijira ta RESF ta yi tsokaci game da batun:

Dokar na fakewa da hujjar jera Faransa da sauran ƙasashen Ƙungiyar Tarayya Turai , ta fannin dokokin ´yan gudun hijira.To amma a zahiri wannan tsabar rashin adalci ne, da ƙyamar baƙi. kuma abin zai haddasa wariya tsakanin faransawa masu yancin ɗaya.

Dokar ta gwamnatin Faransa ta shafi hatta da baƙin da su ka hito daga ƙasashe membobin Ƙungiyar Tarayya Turai.

Idan Majalisa ta amine da ita an tanadi kwanaki 32 zuwa 45 domin tasa ƙeyar mutumen da hukunci ya hau kansa zuwa ƙasar sa ta asuli.

Etienne Pinte dan asulin  Beljiam amma ya na rayuwa a Faransa duk da cewar ya na goyan bayan jam´iya mai mulkin Faransa ya yi Allah da wannan doka:

A ganina wannan doka sama ba ta dace ba,ta sabawa kundin tsarin mulki domin za ta cusa aƙidar bambanci da wariya tsakanin jama´a a lokacin da su ka aikata lefika".

Shi dai Ministan kula da ´yan gudun hijira Eric Besson  ya tsayi kai da fata game da wannan aniya ta sa, kuma ya bayyana dalilin ɗaukar matakin:

Tarayya Turai na buƙatar dokokin bai ɗaya game da al´amuran gudun hijira da neman mafaka, saboda haka, ba za a bar mu a baya ba.Bayan haka, EU za ta tattana da ƙasashen asuli na ´yan gudun hijirar domin gama ƙarfi tare da su, ta hanyoyin cuɗe ni in cuɗe ka.

ƙasar Faransa na daga ƙasashen Turai da su ka fi bada takardar zama ´yan ƙasa ga tsatsan baƙi.

A shekara da ta gabata aƙalla baƙi 136.000 su ka samu wannan takardu, kuma yanzu haka, dubun dubunnai na cikin tsammani.

Hatta  a jiya, saida wasu daga cikin  masu jiran, su ka shirya zanga-zanga gaban Majalisar dokoki, domin buƙatar a gaggauta samar masu da wannan takardu.

Mawallafi: Yahouza Sadisou Madobi

Edita: Umaru Aliyu