1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Girka ta nemi 'yan ƙasar su nuna juriya ga halin da suke ciki.

April 27, 2010

Hukumomin Girka sun buƙaci al'ummar ƙasar su yi haƙuri da sauye - sauyen da suke aiwatarwa.

https://p.dw.com/p/N7zH
Hoto: AP

Frime ministan ƙasar Girka ya bayyana cewar ƙasar sa na buƙatar lokaci domin ɓullo da muhimman sauye - sauyen ga harkokin kuɗin ƙasar gabannin ta fara rage ɗimbin bashin daya yi mata kanta. A lokacin da yake yiwa majalisar dokokin ƙasar jawabi a birnin Athens- yau Talata, George Papandreou ya yi gargaɗin cewar tilas ne al'ummar ƙasar su nuna juriya ga sauye sauyen da hukumomi zasu samar, muddin dai suna buƙatar al'ummomin ƙasa da ƙasa su sake yin na'am da ƙasar.

Sai dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, wadda ta nuna goyon bayan baiwa Girka rancen gaggawa, ta kuma jaddada buƙatar ƙasar ta nuna - a aikace, cewar da gaske take yi. Ƙasar Girka dai ta buƙaci samun rance daga ƙungiyar ƙasashen dake yin amfani da takardar kuɗi ta Euro da kuma asusun bayar da lamuni a Duniya na IMF, wanda yakai na kuɗi Euro miliyan dubu 45. A matsayin ta na ƙasar data fi ƙarfin tattalin arziƙi a ɗaukacin nahiyar Turai, wadda kuma ke yin amfani da takardar Euro, Jamus ce zata samar da mafi yawan rancen da ƙungiyar zata baiwa ƙasar ta Girka.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Zainab Muhammad Abubakar