1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin hadaka ta Jamus ta tabbata

Suleiman Babayo
March 4, 2018

Mambobin jam'iyyar SPD sun amince da shiga cikin gwamnatin hadaka tare da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel lamarin da zai kai ga kafa gwamnati bayan zaben watan Satumba na shekarar da ta gabata ta 2017.

https://p.dw.com/p/2tfO7
Deutschland Ergebnis des SPD-Mitgliedervotums
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

Ma'ajin kudi jam'iyyar ta SPD, Dietmar Nietan ya bayyana sakamakon kuri'un da mamamabobin jam'iyyar ta SPD suka kada a wani taron manema labarai, inda Dietmar Nietan, ya ce a halin yanzu dai komai ya fito fili sannan ya ayyana sakamakon:

"Mambobi 239,604 na jam'iyyar SPD suka amince da shi gwamnatin wajen kada kuri'ar cewa eh, yayin da 123,329 suka nuna rashin amincewa, abin da ke nuna kashi 66.02 cikin 100 sun amince da shiga gwamnatin."

Infografik SPD Mitgliederbefragung GroKo SPA

Wannan mataki mambobin jam'iyyar SPD sun amince da shigar jam'iyyar cikin gwamnatin hadaka tare da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, lamarin da zai share hanya ga Merkel ta jam'iyyar CDU ci gaba da rike madakon ikon kasar ta Jamus wadda ke kan gaba wajen karfin tattalin arziki tsakanin kasashen Tarayyar Turai, wanda a yanzu take iya kafa sabuwar gwamnati domin gunadar da wa'adin mulki na hudu.

Deutschland GroKo-Abstimmungsbriefe in SPD-Zentrale eingetroffen
Hoto: Getty Images/H. Schacht

Ita jam'iyyar ta SPD ta ce wannan mataki ya zama mai tsauri kamar yadda shugaban jam'iyyar na riko Olaf Scholz ke cewa:

"Yanzu an fayyace cewa jam'iyyar SPD za ta shiga gwamnatin Jamus ta gaba. Jam'iyyar ta dauki wannan matakin wanda babu sauki."

Tuni dai Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta mayar da martaki kan yin maraba da sakamakon kuri'un da mambobin jam'iyyar ta SPD suka kada. Amma mutane kamar Kevin Kuehnert shugaban matasa na jam'iyyar ta SPD sun nuna takaicin kan yadda mambobin jam'iyyar SPD suka mika kai wajen sake komawa gwamnatin hadaka da jam'iyyar CDU ta Angela Merkel.