1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

gwamnatin hadin gwiwa a palasdinu

Zainab A MohammadSeptember 11, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5W

Shugaban yankin palasdinawa Mahmoud Abbas yace jammiyarsa ta fatah,da mai na yan hamas mai mulki ,sun cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa,batu da palasdinawan ke fatan zai cire yankin daga halin da take ciki a yanzu ,na takunkumi.

Bangarorin biyu ,kawo yanzu dai sun dauki watanni suna mahawara adangane da kafa gwamnatin hadin gambiza,wanda watakila zai saukaka kallon hadarin kaji da gwamnatin hamas takeywa Izraela a halin yanzu.A jawabin daya gabatar ta gidan talabijin na yankin palasdinawan a yau,shuba Abbas yace bayan lokaci mai tsawo na mahawara,yanzu bangarorin biyu sun cimma yarjejeniya kafa gwamnatin hadin kann kasa.