1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Iraƙi na samun ci-gaba a fannoni da dama

September 9, 2007
https://p.dw.com/p/BuBy

FM Iraqi dan darikar Shi´a Nuri al-Maliki ya ce gwamnatinsa ta samu ci-gaba a bangarori da dama. FM ya yi kira ga kasashe makwabtan Iraqin da su yi aiki tare wajen kawo karshen abin da ya kira wani bala´i da ka iya haddasa rudami a yankin baki daya. Maliki na magana ne a gaban wani taron kasashe makwabtan Iraqi a birnin Bagadaza. Wannan jawabi na sa ya zo ne kwana guda gabanin manyan jami´an Amirka a Iraqi su gabatarwa majalisar dokokin Amirka da wani kiyasi da aka dade ana jira a akan shawarar da shugaba GWB ya yanke na tura karin dakaru dubu 30 zuwa Iraqi. A wani labarin kuma rundunar sojin Amirka ta ce wani farmaki da jiragen saman yakin Amirka suka kai yayi sanadiyar mutuwar wani kusa na kungiyar al-Qaida wanda ya shirya mummunan harin da aka kai kan ´yan kabilar Yazidi wanda ya halaka mutane sama da 400 a cikin watan da ya gabata.