1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Iraqi zata dauki sabin matakan tsaro------

Jamilu SaniJuly 5, 2004

Nan gaba kadan ake sa ran Pm gwamnatin rokin kwarya ta Iraqi zai baiyana irn sabin matakan da zasu dauka na tsaro ------

https://p.dw.com/p/BviS
Hoto: AP

A kasar Iraqi yau litinin ne jami’an sabuwar gwamnatin wucin gadi ta kasar suka sake jinkirta baiyana irin sabin matakan da zasu dauka na shawo kann tashe tashen hankulan dake faruwa a kasar,inda suka soke taron manema labarun da aka shirya gudanarwa yau da nufin bada sanarwar cewar gwamnatin ta Iraqi zata yi afuwa ga yan sari ka noke kuma ta kafa dokar ta bace a wasu sasa na kasar ta Iraqi.

A safiyar yau ne dai aka shirya cewar ministan sharia na Iraqi Malik Dohan al-Hassan da kuma ministan kare hakin bil adama Bakhatiyar Amin zasu gudanar da taron manema labaru,don baiyana irin sabin matakan tsaro da sabuwar gwamnatin wucin gadi ta Iraqi zata dauka na na shawo kann matsalolin da ake fuskanta na rashin zaman lafiya a Iraqi amma kuma aka dage gudanar da wanan taro har sai abinda hali yayi.

Nan gaba kadan ne ake sa ran Pm gwamnatin rikon kwarya ta Iraqi Iyad Allawi zai bada sanarwar irin sabin matakan da gwamnati zata dauka na tabar da doka da odar a fadin kasar ta Iraqi.

Mai magana da yawun Pm Allawi Goreges Sada,ya baiyana cewar a ranar asabar mai zuwa ne ake sa ran gwamnatin Iraqi zata yi afuwa ga yan sari kanoken da suka yaki dakarun taron dangi na Amurka kafin mika ragamar mulki,inda yace sun chanchanci a yi musu afuwa saboda irin matakan da suka dauka a baya na yaki da sojin Amurka dake cikin kasar Iraqi sun yi hakan ne domin kare kansu da kuma kasar su ta haiuwa.

Ciki wata hira da mukadashin ministan tsaron Iraqi Bahram Saleh yayi da gidan talbijin din CNN a jiya lahadi,ya nuna alamun cewar babu wata magana da cewar gwamnatin Iraqi zata yi afuwa ga yan tawaye na kasar,inda yace abin mamaki ne a ce irin wadanan kalami sun fito ne daga bakin mai magana da yawun PM kasar ta Iraqi.

A wani cigaban kuma dan asalin Pakistan din nan da kungiyoyin tsagerun musulmi na Iraqi suka sako,ya baiyana cewar sun yi barazanar yi masa yankan rago.

Dan asalin kasar ta Pakistan Amjad Hafeez,dake yiwa wani kamfanin Amurka aiki a kasar ta Iraqi,ranar juma’ar data gabata ne dai kungiyoyin tsagerun musulmin na Iraqi suka sako shi.

Ya dai baiyana cewar ya sha dukan gaske daga wanda suka yi garkuwa da shi,kuma kasancewar baya iya magana da harshen labarci kungiyoyin tsagerun musulmin na Iraqi sun rika yin magana da shi ne ta hanyar nuna masa alamar cewar zasu halaka nan da kwana uku matakaur dai ba gagauta biya musu bukatun su ba.

A jiya lahadi ne dai aka nuna hotunan Video ta gidan talbijin din Ajazeera inda aka nuna wasu mutane uku a tsaye fuskar su a rufe,suna tsaye a bayan Hafeez a yayin da yake nuna shaidarsa ta inda yake yiwa kamfanin Amurka aiki a kasar Iraqi.

Da yake jawabi kamfanin dilancin labaru na Bernama a yau litinin,PM kasar Malaysia Ahmad Badawi,ya baiyana cewar kasahen musulmi na duniya na duba yiwar aika dakarun su na kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Iraqi,tun da shike a halin yanzu an sami kafuwar gwamnati ta wucin gadi a kasar ta Iraqi.