1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin kasar Masar tace ta ci nasara a kuriar raba gardama

March 27, 2007
https://p.dw.com/p/BuP1

Gwamnatin kasar Masar ta sanarda da cewa ta samu gaggarumar nasara a kuriar raba gardama kann sauye sauye cuikin kudin tsarin mulkin kasar da akayi.

Ministan sharia na Masar Mamdou Marei ya fadawa taron manema labaru cewa duk da cewa kashi 27 cikin dari ne na masu jefa kuria suka kada kuriunsu,amma kashi kusan 76 cikin dari ne suka amince da dokar.

A halinda ake ciki kuma alkalan kasar Masar din sunyi watsi da wannan sakamako na kuriar raba gardamar da suka kira mai cike da zamba,suna masu shan lawashin ba zasu sake sa ido kann zabuka na gaba ba.

Kakakin alkalan Ahmed sabr ya fadawa kamfanin dillancin labaru na AFP cewa sun wanke hannunsu daga wannan sakamako kuma a cewarsa ba zasu sake shiga duk wasu harkoki na abin kunya a kasar ba.