1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Lebanon ta amince da kafa kotun ƙasa da ƙasa na Majalisar Ɗinkin Duniya don yin shari’a kan kisan Hariri.

November 14, 2006
https://p.dw.com/p/Buc9

Majalisar ministocin ƙasar Lebanon, ta amince da wani kundin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta gabtar, na kafa wata kotun ƙasa da ƙasa na musamman, don yi wa waɗanda ake tuhuma da samun hannu a kisan gillan da aka yi wa tsohon Firamiyan ƙasar Rafik Hariri shari’a. A halin yanzu dai an miƙa kundin ne ga kwamitin sulhu na Majalisar don ya amince da shi.

Lebanon dai ta amince da kundin ne duk da rigingimun da aka samu tsakanin ministocin ƙasar, abin da ma ya janyo yin murabus ɗin ministoci 6 masu goyon bayan manufofin Siriya, a cikinsu kuma har da minstoci biyu daga ƙungiyar Hizbulahi. Ana dai zargin jami’an tsaron Siriyan ne da abokan burminsu na Lebanon ɗin da shirya kisan gillan da aka yi wa Harririn a shekarar bara. Amma mahukuntan birnin Damascus na watsi da wannan zargin.