1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin sojin Bama ta kara wa´adin daurin talala ga San Suu Kyi

May 27, 2006
https://p.dw.com/p/Buwb
Gwamnatin mulkin sojin kasar Myanmar wato Bama ta kara wa´adin daurin talala da take yiwa shugabar ´yan adawa Aung San Suu Kyi da shekara guda. Da dai a yau asabar ya kamata a kawo karshen daurin talalan da ake mata a gidan ta. A cikin watan nuwamban bara aka kara wa´adin daurin da watanni 6. Wannan hukunci da gwamnatin ta yanke ya zo ne a daidai lokacin da jam´iyar National League For Democracy ta Aung San Suu Kyi ke bukukuwan cika shekaru 16 da lashe zabukan da aka gudanar a kasar a 1990 da gagarumin rinjaye, to amma gwamnatin sojin ta ki ta amince da sakamakon zaben. A jiya juma´a babban sakataren MDD Kofi Annan ya yi kira kai tsaye ga shugaban gwamnatin soji Janar Than Shwe da ya saki Aung Suu Kyi wadda ta taba samun kyautar zaman lafiya ta Nobel, idan wa´adin daurin talalan da ake mata ya kare a yau.