1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Somalia ta saki jamiin majalisar dinkin duniya da ta tsare

October 23, 2007
https://p.dw.com/p/C15p

Gwamnatin kasar Somalia ta sake jammin hukumar samarda abinci ta MDD bayan kusan mako guda yana tsare.Dakarun tsaro na Somalia da dama ne dai suka kutsa harabar ofishin MDD a birnin Mogadishu ranar laraba da ta gabata suka yi awon gaba da Idris Osman mai kula da rabar da abincin agaji a cikin birnin na Mogadishu.Jamian gwamnati sunce suna binciken Osman kann wasu laifuka da basu baiyana su ba.Tsare Osman ya janyo suka ga gwamnatin Somalia daga kasashe da dama.