1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Somalia ta shawo kan rikicin Mogadishu

April 26, 2007
https://p.dw.com/p/BuMk

P/M Somalia Ali Mohammed Gedi ya sanar da cewa dakarun sojin gwmnati sun sami nasarar fatafakar yan Islama a birnin Mogadishu, bayan ɗauki ba daɗi da aka kwashe tsawon kwanaki tara ana gwabzawa. Yace a yanzu an shawo kan dukkan wata tarzoma a birnin, sai dai rahotanni sun baiyana cewa an jiwo amon harbin bindigogi dana igwa a kudancin birnin na Mogadishun. P/M Gedi yace yan Somaliya su kimanin 340,000 waɗanda suka yi ƙaura daga gidajen su sakamakon kazamin faɗan mafi muni da aka taba gani a birnin tun shekaru 15 da suka wuce, a yanzu suna iya komawa gida. Bugu da ƙari yace sojojin gwamnati da aminan su na ƙasar Habasha sun kame wani yanki mai girma na yan tawayen a arewacin Mogadishu yana mai cewa yan tawayen fiye da 100 suka miƙa wuya.