1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Sri-Lanka ta yi tayin shawarwari ga yan tawayen Tamoul Tigers.

February 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuSW

Shugaban ƙasar Sri Lanka Mahinda Rajapkase, yayi tayi ga yan tawayen Tamouls Tigers na wannan ƙasa, zuwa sabin shawarwarin zaman lahia.

A makon da ya gabata, ƙasashe masu baiwa Sri Lanka tallafi, su ka shirya zaman taro, inda su ka yanke shawara cewa, gwamnatin Colombo, ta raba madafan mulki, tare da yan tawayen, idan kuma ta hau kujera na ƙi, ƙasashen sun yanke agajin da su ke ba Sri lanka.

An sha ganawa tsakanin ɓangarorin 2, ba tare da cimma sulhu ba, ganawar ƙarshe ta wakana a watan wataba oktober na shekara da ta gabata, saidai a ka watse baram-baram.

Yan tawayen Tamoul Tigers, na bukatar girka ƙasa mai cikkaken yanci, a yankin arewa maso gabacin Sri-Lanka, matakin da gwamnati ta ƙi amincewa da shi.