1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Sudan ta yi watsi da shawara AU ta tura dakarun majalisar ɗinkin dunia a yankin Darfur

February 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6s

Gwamnatin ƙasar Sudan, ta tsawata wa ƙungiyar tarayya Afrika da, ta daina yi mata shiga sharo ba shanu ,a harakokin ta na cikin gida.

Ministan cikin gida na ƙasar Al Zubeir Beshir Taha, ya bayyana hakan, a wani taron mane,ma labarai day a shirya jiya a birnin Khartum.

Ministan yace ƙungiyar tarayya Afrika ba ta da yanci gayyato sojojin Majalisar Ɗinkin Dunia a yankin Darfur.

Yayi hakan domin maida martini ga hukumar zartaswa ta AU da ta buƙaci Majalisar ɗinkin Dunia, ta aika dakarun ta a yankin Darfur.

A sakamakon wannan bukata, shugaba Bush na Amurika a makon da ya gabata ya bada goyan baya.

A ɗaya gefen ministan harakoki ciki gidan Sudan ya zargi Isra´ila da hannu a cikin rikicin yankin Darfur ta hanyar bada makamai ga yan tawaye.