1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Sudan za ta biya diyya ga alúmar Dafur

October 4, 2007
https://p.dw.com/p/Bu9X

Shugaban ƙasar Sudan Hassan Omar al-Bashir yayi alƙawarin biyan dala miliyan 300 a matsayin diyya ga yankin Dafur da yaƙi ya yiwa kaca-kaca. Tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter ya baiyana hakan bayan ganawa da shugaba al-Bashir. Carter yace ya al-Bashir ya tabbatar musu a tattaunawar da suka yi da shi da Archbishop Desmond Tutu cewa zai biya wannan diyya ga alúmar Dafur. Yace gwamnatin Sudan za ta samar da dala miliyan ɗari ɗaya yayin da ragowar miliyan ɗari biyun kuma za ta samo su ne rance daga ƙasar China.