1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Thailand ta fa'ɗaɗa dokar ta ɓaci zuwa wasu sassan ƙasar

May 13, 2010

Jami'an tsaron Thailand sun yi taho mu gama da 'yan adawar ƙasar.

https://p.dw.com/p/NN4Z
Hoto: AP

Gwamnatin Thailand ta fa'ɗaɗa dokar ta ɓacin data ƙafa a wasu sassan ƙasar ya zuwa larduna 17, domin hana mazauna yankunan karkara damar shiga cikin masu zanga zangar nuna adawa da gwamnatin ƙasar. Wannan matakin dai shi ne na baya bayannan cikin matakan da hukumomin ƙasar ke ɗauka da nufin daƙile masu zanga zangar nuna adawa da gwamnatin, waɗanda hatta a ɗazunnan, suka yi taho mu gama da jami'an tsaro, wanda kuma ya janyo mutuwar ɗaya daga cikin masu adawar dake sanye da ja'ja'yen riguna.

Wannan dokar dai ta fa'ɗaɗa hurumin da sojojin ke dashi na kawar da masu jerin gwanon, da kuma taƙaita harkokin ƙungiyoyin kare haƙƙin fararen hula. Kakakin gwamnatin Thailand Panitan Wattanayagom ya ce dokar ta ɓacin na da nufin hana ƙarin talakawa damar zuwa Bangkok ne domin shiga cikin zanga zangar.

A halin da ake ciki kuma ofisoshin jakadancin ƙasashen Amirka da Birtaniya da kuma Holland sun bayar da sanarwar dakatar da aikin su gobe jumma'a - idan Allah ya kaimu, a yayin da suma hukumomin Thailand ɗin suka buƙaci kamfanoni su baiwa ma'aikatan su hutu - a yunƙurin ɗaukar matakan shawo kan matsalar masu zanga - zangar, waɗanda suka ce ba zasu taɓa miƙa wuya ba.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Yahouza Sadisou