1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

GwamnatinEthiopia ta yi kira ga hukumar REd Cross ta fita daga yankin Ogaden

July 25, 2007
https://p.dw.com/p/BuFX

Gwamnatin ƙasar Ethiopia, ta yi kira ga hukumar bada agaji ta Red Cross, ta fita daga yankin Ogaden dake gabacin ƙasar, nan da kwanaki 7.

Hukumomin Adis Ababa na zargin Red Cross da yin katsa landan, a harakokin siyasa, a wannan yanki.

Kakakin fadar gwamnatin yankin Jema Ahmed Jema, ya ce hukumar Red Cross na wuce gona da iri, wajen shiga sharo ba shanu, ta fannin yaɗa labaran ƙage, a game da al´ammuran da ke gudana a yankin Ogaden.

Ogaden na ɗaya daga yankunan Ethiopia da ke fama da tashe-tashen hankulla ,a sakamakon fito na fiton da a ke gwabzawa, akai a kai tsakanin dakarun gwamnati, da dakarun ƙungiyar tawaye ta ONLF.

A watan juli da mu ke ciki, hukumar kare haƙƙoƙin bani adama, ta Human Right Watch, ta zargi hukumomin Ethiopia da kai hare hare, a garuruwa da dama, na yankin Ogaden, wanda a sakamakon su mutane da dama, su ka kwanta dama.