1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gyaran kundin tsarin mulki a Moritaniya

Gazali Abdou Tasawa
August 7, 2017

Sakamakon zaben raba gardama da aka gudanar a jiya Lahadi a kasar Moritaniya kan shirin yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima ya nunar da cewa al'umma ta amince da shirin da gagarimin rinjaye. 

https://p.dw.com/p/2hn7q
Mauretanien Präsident Mohamed Ould Abdel Aziz
Hoto: Getty Images/AFP

Shirin yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulki wanda shugaban kasar ta Moritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz ke son yi ya tanadi soke majalisar dattijai tare da maye gurbinta da ta wakillan yankuna da kuma sauya fasalin tutar kasar ta hanyar kara wasu jajayen launuka biyu a samanta da nufin karrama kushewar abin da gwamnatin ta kira shahidai na kasa wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen kalubalantar mulkin mallakar da Faransa ta yi wa kasar wanda kawo karshe a shekara ta 1960. Sai dai tuni kawancan jam'iyyun adawar kasar wanda da ma ya yi kira ga magoya bayansa da su kauracewa zaben ya yi watsi da sakamakon nasa.