1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

May 11, 2009

Kamfanin Spie Batignolles ya zargi kamfanin Bilfinger Berger da zaluntarsa a Nijeriya.

https://p.dw.com/p/HnjL
Kamfanin mai na Ghana GOILHoto: Stefanie Duckstein

A yau zamu fara ne da taƙaddamar da ake fama da ita tsakanin wani kamfanin ƙasar Faransa da kamfanin gine-ginen nan na Bilfinger Berger, wanda kamfanin Faransar ke zarginsa da zaluntarsa akan wasu maƙudan kuɗi na cin hanci a Nijeriya. A lokacin da take rawaito wannan rahoto jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:

Bilfinger Berger Deutscher in Nigeria entführt
Hoto: AP

"Wannan taƙaddamar 'yar shekaru goma ta samo asali ne daga shekara ta 1996. A wancan lokaci kamfanin Bilfinger ya shiga haɗin guiwa da kamfanin Faransa na Spie Batignolles domin gina wani babban bututu na gas a Nijeriya. Tun bayan wannan lokaci Bilfinger, wanda reshensa na Julius Berger ke gudanar da ayyukansa a Nijeriya, ya riƙa neman wasu kuɗaɗe ba tare da wani bayani a game da hanyoyin da za a yi amfani da su ba. Kamfanin na Faransa dai yayi imani ne cewar kamfanin Bilfinger yayi amfani da waɗannan kuɗaɗe ne don ba da toshiyar baki a Nijeriya."

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland rahotanni guda biyu ta bayar dangane da haƙar ma'adinai a ƙasashen Ghana da Nijer, inda ta saka ayar tambaya a game da ire-iren albarkatun da Allah Ya fuwace wa ƙasashen Afurka ko shin alheri ne ko kuwa bala'i ga ƙasashen. Dangane da Nijer dai jaridar cewa tayi:

Abwrackpraemie bei Autos Konjunktur
Hoto: AP

"Kawo yanzu babu wani alfanu da ƙasar Nijer ta samu daga arziƙin Uranium da Alla Ya fuwace mata. A maimakon haka kamfanonin sarrafa atom na ƙasashen Faransa da China ne kawai ke cin gajiyar wannan ma'adani mai muhimmancin gaske ta fuskar tsaro."

A game da Ghana kuwa jaridar ta ce:

"Duk da adawa ta ƙasa da ƙasa dake fitowa daga sassa daban-daban na duniya babban kamfanin haƙar ma'adinan nan na Newmont ya samu izinin haƙar zinare a cikin ɗaya daga dazuzzukan kurmin da suka yi shaura a ƙasar Ghana. Wannan aikin zai ɓannatar da abin da ya kai eka 74 na dazuzzukan kurmin da tada ƙauyuka da dama dake yankin na Ajenjua Bepo a jihar gabacin Ghana."

Symbolbild Medien in Niger
Hoto: DW/Bilderbox.com

Wata sabuwar manufa ta gwamnatin Jamus ta ƙiƙiro baya-bayan nan a game da ba da ladar da ta kai ta Euro dubu biyu da ɗari biyar ga duk wanda ya kai tsofuwar motar da yake mallaka don a lalata ta na neman yin cikas ga wata kasuwa mai samar da ƙazamar riba a nahiyar Afurka. Wannan shi ne kanun wani rahoto da jaridar Financial Times Deutschland ta buga, inda take cewar:

"A halin yanzu haka kimanin Jamusawa miliyan ɗaya da dubu ɗari biyar ne suka gabatar da takardun neman cin gajiyar wannan manufa, wadda take nema ta kassara cinikin motocin gwanjo zuwa Afirka. Domin kuwa ƙasar ta Jamus ita ce akan gaba inda akan fitar da motocin gwanjo kimanin dubu 100 daga ƙasar zuwa sassa daban-daban na Afurka a shekara. A sakamakon wannan lada da gwamnati ta ware mutane sun fi sha'awar karɓar wannan zunzurutun kuɗi na euro dubu biyu da ɗari biyar a maimakon sayar da motar akan farashin da bai zarce euro 400 kacal ba."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammad Nasiru Awal