1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haɗin-gwiwar sojojin Koriya ta Kudu da na Amirka

Halimatu AbbasAugust 16, 2010

Sojojin Amirka da na Koriya ta Kudu sun fara wani atisayin haɗin-gwiwa

https://p.dw.com/p/OoTI
Tankokin atilari na sojan Koriya ta Kudu da AmirkaHoto: AP

Sojojin ruwa na ƙasashen Koriya ta Kudu da na Amirka sun fara wani sabon atisayi, na haɗin-gwiwa wanda ya haɗa sojoji dubu 56000 na Koriya ta Kudu da kuma soja dubu 30000 na Amirka. Mininistan tsaro na ƙasar Koriya ta Kudun wanda ya shaida cewa za a ƙwashe tsawon ƙwanaki goma ana gudanar da atisayin, ya ce ya na zaman wata kariya ga barazanar da Koriya ta Arewa ke shirin yin ga ƙasahensu.

Ƙasar dai ta Koriya ta Arewa wacce ta kira wannan atisayi na soja da sunan mamaya mafi girma , ta ce za ta ladabtar da ƙasar Amirka da kuma Koriya ta Kudu fiye da yadda basu taɓa gani ba na ramuwar gayya a duniya. A wani jawabi da ya yaɗa ta shafin intanet na soja, babban kwamandan dakarun Amirka a ƙasar Koriya ta Kudu, Janar Walter Sharp ya bayyana atisayin da cewa shi ne irinsa mafi girma da aka taɓa yi a duniya.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita: Halima Balaraba Abbas