1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haɗin kai tsakanin Jami´an tsaro da Limaman addinin Musulunci ya shinfiɗa zaman lahia a unguwar Katernberg dake Essen a Jamus.

Yahouza Sadissou MadobiNovember 21, 2007

Tuntubar juna tsakanin Jami´an tsaro da Maluman addinin Musulunci ta haifar da zaman lahia a wasu yankunan Jamus

https://p.dw.com/p/CQ3V
Limamin Masallaci da Dan JaridaHoto: DW/Scheschkewitz

A birnin Essen dake yankin Nordreihn Westfaliyana Jamus, jami´an tsaro da limaman addinin musulunci sun haɗa ƙarfi domin tabbatar da mu´amila ta cuɗe ni in cuɗe ka, tsakanin baƙi yan kaka gida da ke birnin da sauran jama´a.

A sakamakon wannan haɗin gwiwa sun cimma gagaramar nasara wadda ta zama abun koyi ga sauran sassan ƙasar Jamus.

Akwai wani yanki na mussaman a birnin Essen, wanda aka raɗawa suna Katernberg.

Wannan unguwa ta ƙunshi baƙi ´yan kaka gida, daga yankunan dabam-dabam na duniya musamman Marroko, Libanon, da Turkiya.

Mafi yawan baƙin unguwar musulmi ne. Da farko anyi ta samun tashe-tashen hankula da rashin fahintar juna tsakanin su da jama´a, a game da haka limaman unguwar, tare da ´yan sanda, su ka ƙirƙiro wani shiri na musamman wanda ya ƙudurci samar da kwanciyar hankali da kuma cuɗe ni- in- cuɗe ka, tsakanin mazauna unguwar baki ɗaya.

Hebert Czarnyan, wani ɗan sanda ne, dake unguwar Katernberg, ya bayayana cewar mussabbabin da ke hadasa tashe-tashen hankula, sun haɗa da rashin aikin yi, na matasa da kuma fatara da talauci, da ´yan kaka gidan ke fama da su.

A sakamakon haka, da dama daga matasa suka shiga shaye- shaye.

Kashi 50 cikin 100 na matasan unguwar ´yan ƙasa da shekaru 20 ne, kuma mafi yawansu suna anfani da takardun zama ƙasa na wucin gadi.

Wannan unguwa na da masalaitai gudu uku, ɗaya na ´yan ƙasar Libanon, sai kuma 2 na Turkawa.

Herbert Czarnyan, ya tuna lokacin da ya fara zuwa wajen wani limami , domin ya roƙe shi haɗin kai a game da batun tsaro a unguwar:

Yace a shekara ta 1997 ne mu ka fara samun haɗin kai wajen limamin.

Hakan ya biwo bayan wani rikici da ya faru, a iyakar unguwar Katernberg da ta Schönebeck, inda a ke gudanar da hada-hadar kasuwanci mai yawa.

Ta la´akari da barazanar da jama´a ke fuskanta, sai na sami ɗaya daga ´yan kasuwar Libanan, inda na tambaye shi ra´ayinsa, a game da hanyoyin samar da kwanciyar hankali, anyi katari, a lokacin, limamin masalacin „Salahadin“ dake unguwar na zaune.

Sai shima ya bada shawara, to daga nan fa, sai muka ci gaba da tuntuɓara juna.

Matakin da jami´an tsaro da kuma limamin unguwar suka ɗauka yayi tasiri matuƙa gaya.

Limamin na tattara musulmin unguwar, domin faɗakar da su a game da hanyoyin samar da zaman lahia.

Lokaci zuwa lokaci, su na tantanawa, a game da matsalolin aikin yi na matasa, da kuma dubarorin hana su shiga shaye-shaye.

Shekaru 2 bayan samun haɗin kai daga limamin masalacin yan Libanon, shima limamin babban masalacin Turkawa Halit Pismek, ya bada tasa gudummuwa, ta fannin shawarwari da jami´an tsaro, da zumar tabbatar da kwanciyar hankali a unguwar Katernberg.

A halin da ake ciki, rahotanin jami ´an tsaro sun nunar da cewar, an sami gagaramar nasara wajen raguwar tashe-tashen hankula, mussamman a ɓangaren matasa, a sakamakon wannan mataki na haɗin gwiwa.

Ga masu nuna ɗari-ɗarin ga wannan mu´amila, Liman Halit Pismek, ya ci gaba da faɗakar da su.

Babban komishinan yan sandar Essen, Frank Matuszek, ya bayyana gamsuwa a game da yadda suka cimma nasara shinfiɗa kwanciyar hankali tare da haɗin kan malamuman addinin Islama.

Sannan ya kyauatta zaton wannan haɗin kai ya dawwama.

Nasara da aka samu a Essen, ta zama abin koyi a Jamus baƙi ɗaya.

Jami´an tsaro a birane kamar su Munich, sun bayyana girka wata ƙungiyar tare da yin dogaro da tsarin Essen.

Sannan Halit Bismek, Limamin babban masalacin Turkawa na Essen, ya kai rangadi a Berlin bisa gayyatar hukumomin birnin na tarayya , inda yayi bayyanai ga takwarorinsa limamai, a game da hanyoyin da su ka bi a Essen ,domin samar da fahintar juna, tare da ragewa matasa musulmi zaman kashe wando, da kuma tashe -tashen hankulla.

Ita da kanta gwamnatin tarayya ta yi yabo na mussamman ga tsarin da jami´an tsaro, da kuma muluman musulunci su ka ɓullo da shi a birin Essen.

Ministan cikin gida Wölfganf Schäuble, ya bayyana aniyar gwamnati ,ta faɗaɗa ire-iren wannan tsari ,da zumar cimma burin ƙarfafa mu´amila da zamantakewa, tsakanin al´umomomi ,ƙabilu,Al´adu, da addinai dabam-dabam da ke zaune a nan ƙasar Jamus.