1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomi na kame mutane sakamakon dokar tabaci a Habasha

Salissou Boukari
November 12, 2016

Bayan kafa dokar tabaci a farkon watan Oktoba da ya gabata kawo yanzu, kwamitin da ke sa ido kan dokar da aka ayyana, ya sanar cewa sun kai ga kama mutane fiye dubu 11 bisa zargin laifuka daban-daban.

https://p.dw.com/p/2SbcC
Äthiopien Regierung Soldaten ARCHIV
Hoto: picture alliance/AP Photo/ltomlinson

Cikin wata sanarwa ce dai da ya fitar, shugaban kwamitin da ke bi sau da kafa dokar tabacin, Taddesse Hordofa, ya ce sun kama mutane dubu 11 da 607 kuma an rarrabasu a cikin gidajen firsina shida na kasar. Cikinsu akwai mata 347 bisa laifin taka dokokin da yawa na kasa, da suka hada da neman tada zaune tsaye, lalata kayan jama'a, ko kuma kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa ta hanyar saka shinge kan hanyoyi.

A cewar kungiyoyin kare hakin dan Adam na kasar ta Habasha, an kama mutane da dama a yankin Oromo da ke tsakiyar kasar, da na Amhara da ke arewaci, inda ake samun masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin kasar tun yau da shekaru 25 da suka gabata, wanda kuma amfani da karfin da jami'an tsaro ke yi a kan su ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane.