1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha: Zanga-zanga kan mutuwar mutane

October 3, 2016

Wata zanga-zanga ta barke a kasar Habasha kwana guda bayan da mutane da dama suka rasu a wani turmutsutsu da aka yi lokacin da 'yan sanda suka yi arangama da masu kyamar hukumomin kasar.

https://p.dw.com/p/2QqDj
Äthiopien Anti-Regierungs-Protesten
Hoto: REUTERS/T. Negeri

Shaidun gani da ido suka ce mutane ne da dama suka fantsama kan titunan Ambo da  Bule Hora da sauran garuruwa da ke Oromiya don nuna fushinsu biyo bayan rashin da aka yi a jiya Lahadi. Wani dalibin jami'a da ya zabi a sakaya sunansa ya ce ya ji harbe-harbe lokacin da ake zanga-zangar kafin daga bisani komai ya lafa, inda ya kara da cewar daga baya titunan a Ambo sun kasance ba kowa a kansu kana sanan lamura sun tsaya cik. A wasu yankunan kuma mazauna wuraren sun bada labarin arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro sai dai ya zuwa babu labari da aka samu na asarar rai.