1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin murkushe kungiyar IS

Lateefa Mustapha Ja'afarNovember 27, 2015

Kasashen Faransa da Rasha sun sha alwashin hada karfi waje guda domin yakar kungiyar 'yan ta'addan IS da ke son ta addabi duniya baki daya.

https://p.dw.com/p/1HDKE
Shugaban Rasha Vladimir Putin da na Faransa Francois Hollande
Hoto: Reuters/M. Klimentyev

Yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a Moscow, shugabannin kasashen biyu François Hollande na Faransa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun bayyana cewa tilas ne sai al'ummomin kasa da kasa sun hada kai wuri guda domin kawo karshe ayyukan kungiyar ta IS. Saidai an kasa samun daidaito a tsakaninsu dangane da batun saukar shugaban kasar Siriya Bashar Al-Assad daga kan karagar mulki, inda Shugaba Hollande na Faransa ya dage kan sai Assad ya sauka daga matafun iko Putin kuwa ke cewa lallai za a iya fatattakar 'yan IS ne kawai da sojojin kasa kuma ya zama tilas a hada kai da Shugaba Assad. Dangane da harbo jirgin yakin Rasha da sojojin Turkiya suka yi kuwa shugabannin biyu sun bayyana bukatar kaucewa sake afkuwar hakan a gaba. Shugaba Putin na Rasha ya ce:


"A tunaninmu akwai bukatar a hada kai sosai domin mu samu kwarin giwawar da ta dace, amma idan takwarorinmu basu shirya ba kamar yadda na bukata a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, to ba matsala Moscow za ta gudanar da aikin ta hanyar da take ganin ta dace."