1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadarin ambaliyar ruwa a kudancin Asia---

Jamilu SaniJuly 26, 2004

Hukumomin kasahen kudancin Asia sun tashi tsaye wajen taimakawa mutanen da hadarin ambaliyar ruwa ya ritsa da su--

https://p.dw.com/p/Bvhn
Hoto: AP

Rahotanin dake fitowa daga yankin kudancin kasahen Asia,sun baiyana cewar a halin yanzu ana cigaba da samun karuwar yawan mutanen da suka rasa rayukan su a sakamakon ambaliyar ruwan data afku a wanan yanki,inda a aka baiyana cewar kawo yanzu mutane miliyan 923 suka rasa rayukan su ko kuma suka rasa matsugunan su na asali a sakamakon afkuwar wanan ambaliyar ruwa.

A yau litinin ne dai aka baiyana cewar gwamnatin India ta aika maikatan bada agaji zuwa yankunan da aka fi fama da matsaloli na ambaliyar ruwa don kai kayayakin agaji,a yayin kuma da ak baiyana cewar matsalolin ambaliyar ruwa sun shafi kashi biyu daga cikin uku na kasar Bangaladesh.

Koda yake matsalolin na ambaliyar ruwa da farko sun fi shafar yankin arewa maso gabashin India,to amman kuma matsalolin na ambaliyar ruwa a halin yanzu sun fi shafar Bangaladesh,inda aka baiyana cewar matsalolin na ambaliyar ruwa sun tilastawa duban mutane yin kaura daga gidajen su tare da neman wurin fakewa a karkashin inuwar bishiyoyi ko kuma tantuna.

Kimanin mutane miliyan 12 a India,miliyan 30 kuma a Bangaladesh suka yi asarar matsugunan su na asali,tun bayan da ambaliyar ruwa ta barke a farkon damunar bana data fara tun daga tsakiyar watan yunin da ya gabata a yakin na kudancin Asia.

Yawan mutane da suka mutu ko kuma suka bace a sakamakon bular matsalolin na ambaliyar ruwa a India ya kai 535,sai kuma 285 a kasar Bangaladesh,yayin da mutane 86 suka rasa rayukan su a kasar Nefal,sai kuma kasar Afghanistan mai yawan mutane 16,uku kuma a Buhtan,kamar yadda kamfanin dilancin labaru na AfP ya gudanar da bincike na yawan mutane da suka mutu a sakamakon matsaloli na ambaliyar ruwa a yakin kudancin Asia:

Rahotanin dake fitowa daga kafafan yadda labaru na yankin kudancin Asia sun nunar da cewar yawan mutane da suka raya rayukan su sakamakon hadarin ambaliyar ruwa a yankin na kudancin Asia na iya cigaba da karuwa ta la’akari da yadda ake cigaba da samun zubar ruwan sama kamar da bakin kwarya.

A Dahka baban birnin kasar Bangaladesh hukumomin kasar sun baiyana cewar mutane 124,000 matsaloli na ambaliyar ruwa suka tisatawa kaurawcewa gidajen su,inda suka nemi mafaka a cibiyoyin da hukumomin kasar suka tanadar don tsugunar da mutane da hadarin ambaliyar ruwa ya ritsa da su.

A India kuma mutane 535 aka baiyana cewar sun rasa raukan su,a yayin da matsaloli na ambaliyar ruwa suka mamaye yankunan karkara na kasar makoni biyun da suka gabata.

A kasar Bangaladesh wata wasu kungiyoyi na bada agaji sun bukaci gwamnati ta samar da jirage masu saukar ungulu don gudanar da aiyuka na bada agaji.

A halin yanzu dai kasahen dake fama da matsaloli na ambaliyar a yanki na kudancin Asia sun fara samun taimako na kudade,inda a halin yanzu ofishin jakadancin Birtania a Bangaladesh ya baiyana cewar Birtania ta bada taimako na Fam milyan goma,don taimakawa murtanen da hadarin ambaliyar ruwa ya ritsa da su.