1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadarin jirgin sama a Irkutsk

July 9, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6F

Goma sha daya daga cikin pasinjoji da suka rasa rayukansu a hadarin jirgin saman daya fadi a Siberia da safiyar yau lahadi,baki ne yan kasashen ketare.Jamiai sun sanar dacewa akwai yan kasar Poland guda biyu da jamusawa biyu da yan Moldovans biyu da yan koriya ta kudu biyu kana da sinawa guda uku.Bugu da kari jirgin na kuma dauke da kanan yara guda 14,wadanda shekarunsu ya kama daga 12 zuwa kasa.Akalla mutane 137 ne suka rasa rayukansu,daga cikin mutane 200 dake cikin jirgin na Airbus A310,dayayi hatsari ayayinda yake sauka a filin saukan jiragen sama na Irkutsk.Sai dai kawo yanzu jamiai basu sanar da halin da ake ciki dangane yan kasashen ketare da yara da suka rasu ba.