1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haddar abubuwa

Abba BashirMay 22, 2006

Saurin bijiro da abin da aka daddace

https://p.dw.com/p/BvVR
Al-kur'ani Mai girma
Al-kur'ani Mai girmaHoto: DW

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malam Nura Zaharadden Khamis ,Azare a jihar Bauchin Tarayyar Najeriya. Malamin ya ce .Don Allah ku sanar da ni ,shin, wane mutum ne a wannan Duniya ya fi kowa iya haddace abu a kwakwalwarsa, da kuma saurin bijiro da abin da ya haddace a duk lokacin da aka tambaye shi?

Amsa: Tirkashi, babbar magana, to malam Nura a iya binciken da muka yi mun gano cewa , wani bawan Allah da ake kira da suna Muhammad Ali Halici, dan Kasar Turkiya, shine Mutumin da Duniya ta zaba a matsayin mutumin da ya fi kowa iya hadda da kuma saurin bijiro da abin da ya haddace din, an ko yi wannan zabe ne tun a shekarar 1967.

Shi dai Muhammad Ali Halici, a ranar 14 ga watan Oktoban 1967 ya karanta Alkur’ani mai girma tun daga Bakara har Nasi da hadda , kuma a cikin awa shida kacal,wanda kuma Al-kur’ani ya kunshi surori guda 114 da koma ayoyi 6,666. Kuma manyan Malamai shida na Al-kur’ni mai gima ne suka bi wannan karatu, suka fede shi, suka kuma tabbatarwa da Duniya cewa , karatun ya cika dukkanin ka’idoji na wajibi da ake bukata wajen karatun Al-kur’ni mai tsarki.

To sakamakon haka aka ce wannan hadda da Muhammad Halici ya yi, shine tunani mafi sauri na kwakwalwa,da kuma saurin bijiro da wani abu da kwakwalwa ta taba rikewa, wanda Duniyar kimiyya ta taba sani a tarihin wannan zamani.

Da fatan mai sauraron namu ya gamsu da wannan takaitacciyar amsa da muka bashi.