1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin ilimi kalubalen mabiya addinai a Najeriya

Muntaqa Ahiwa/YBJanuary 8, 2016

A kokari da take yi don tabbatar da zaman lumana da fahimtar addinai a Najeriya, hadin gwiwar Iklisiyoyin Najeriya TEKAN ta shirya taro don kauce wa gurbatacciyar koyarwa ta addini.

https://p.dw.com/p/1HaU6
Interfaith Mediation Centre in Kaduna
Malamai na addinin Islama da Kirista da ke son hadin kan junaHoto: Katrin Gänsler

Kungiyar TEKAN mai mambobi akalla miliyan 22 a fadin kasar Najeriya, taronta na bana da ke zama karo na 62 tun kafuwarta a shekara ta 1955, ta yi shi ne a garin Numan da ke kudancin jihar Adamawa da zimmar tabbatar da jama'a bisa koyarwar nassin masihiyya, tare da kira ga su ma mabiya addinin Islama da su dauki salon don kauce wa rudanin da wasu ke haddasawa da sunan addini.

An dai yi ittifakin cewa, karancin ilimin addini shi ke baiwa wasu masu mugwayen akidu damar cusa munanan hudubobi a zukatan wasu da dama, abin da ya bayyana a zahiri inji jagoroin addinan da suka halarci taron da tushen tashin fitintinu a Arewa maso Gabashin Najeriya da ma wasu sassa na duniya.

Interfaith Mediation Centre in Kaduna
Mahalarta taron hadin kan Musulmi da KiristaHoto: Katrin Gänsler

Haka nan ma taron ya aibanta shugabannin siyasa, da yin biris da hakkoki na jama'a da ke kawunansu, inda akasari suke daukar matsalolin addininai tamkar basa cikin wajibansu.

Jagororin taron sun amince cewa ci gaba da fadakar da jama'a tare da kiyaye hakkoki yadda ubangiji ya umurta, za su taimakawa nasarar samun zaman lafiya da fahimtar juna.