1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haiti: An samu karuwar salwantar rayuka a farkon 2024

April 20, 2024

Mutane fiye da 1,6000 ne suka mutu a Haiti a farkon shekarar 2024 sakamakon tashe-tashen hankula.

https://p.dw.com/p/4f08z
Wadanda suka mutu Haiti sun karu a shekarar 2024
Wadanda suka mutu Haiti sun karu a shekarar 2024Hoto: Ralph Tedy Erol/REUTERS

Alkalumman Majalisar Dinkin Duniya sun yi nuni da cewa, tashe-tashen hankula a Haiti ya salwantar da rayukan mutum fiye da 1,600 yayin da wasu 850 suke jikkata a cikin watanni ukun farko na wannan shekarar ta 2024. A cikin rahoton da Majalisar ta fitar, ta ce wannan adadin ya karu da kashi 50 cikin 100 idan aka kwatanta da zangon karshe na shekarar da ta gabata.

Karin bayani:Fargabar dagulewar al'amura a Haiti

Ana dai samun mutuwar mutum hudu cikin biyar ne a babban birnin kasar Port-au-Prince inda hukumomi ke kokarin samun cikakkken iko da shi.

Kungiyoyin miyagu dai ke iko da yawancin yankunann birnin. A watan Fabarairun shekarar 2024 ce dai kungiyoyin suka ce suna fafutukar hambarar da gwamnatin kasar da ba a zabe ta ba.

An dauki tsawon makwanni kafin kafa majalisar rikon kwarya domin shawo kan dambarwar siyasar kasar da ma shirya gudanar da zabe. Tun dai shekarar 2016, rabon da kasar Haiti ta gudanar da zabe.