1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HALIN DA AKE CIKI A AFGANISTAN BAYAN HARI......

ZAINAB AM ABUBAKARDecember 29, 2003
https://p.dw.com/p/Bvms

Sauran burbudin yan rusasshiyar mulkin Taliban a kasar Afganistab sun rataya alhakin harin kunar bakin wake daya kashe mutane bakwai jiya a kusa da filin saukan jiragen sama dake birnin Kabul,kana sun lashi takobin cigaba da kai ire iren wannan hari a sassa daban daban na kasar.Harin na jiya a Kabul dai ya kasance mafi munin irinsa tun bayan wani hari daya kashe sojojin jamus 4 tare da raunana mutane 31,ayayinda a hannu guda ake kokarin kaddamar da sabuwar kundun tsarin mulkin kasar.

Kasashen yammaci dai sun kurawa wannan taro ido wanda ya shiga mako na uku,duk dacewa ana samun jinkiri daga bangaren masu tattaunawa wadanda suka kasance yan majalisar Loya Jirga.Tuni dai mayakan na Taliban suka kaddamar da jihadi kann dakarun kasashen waje dake Afganistan,baya ga barazanar kashe wakilan taron da sukayi.

Mataimakin commandan rundunar Taliban Mullah Sabir Momin yace akwai yan yakin sunkuru sama da 200 a birane daban daban na kasar,ayayinda cikin birnin Kabul kadai akwai kwararru da akayi musu horo na musamman domin kunar bakin wake,wadanda kuma na iya kera boma bomai masu karfi da albarkatu kalilan.Yayi wannan bayanai ne ta wayan tafi da gidanka na Satelite,wanda idan ya kasance gaskiya ne wadannan sabbin hanyoyi na kai hari,zai zama wani sabon kalubale wa sojojin kiyaye zaman lafiya 5,700 dake Kabul,banda rundunar Amurka mai sojoji kimanin dubu 12 dake neman burbudin yan Taliban da yan Al Qaeda.

Daga watan Augusta zuwa yanzu sama da mutane 400 suka rasa rayukansu acigaba da harin da yan Taliban din ke kaiwa.A harin na jiya dai Jamian tsaro 5 suka gamu da ajalinsu,tare da yan kunar bakin waken biyu.A halin da ake ciki dai yansandan Afganistan tare da sojojin kiyaye zaman lafiya sun kaddamar da bincike kann wannan hari da aka kai jiya.

A dangane da zaman mahawara kann gyaran kundun tsarin mulkin kasar wanda ya shiga rukuni na karshe ayau litinin,dangane da irin mulki daya dace a tafiyar a Afganistan.Dukkan wakilai 502 ke halartan zaman na yau,inda ake fuskantar rarrabuwan kawuna.

To sai dai a hannu guda kuma,Afganistan ta aike da agajin dala dubu 150 wa kasar Iran da ke makwabtaka da ita,a matsayin agaji ,dangane da girgizar kasa daya kashe mutane kimanin dubu 25 a wannan kasa.Tuni aka mikawa gwamnatin Iran tsabar dala dubu 100,ayayinda shugaba Hamid Kharzai na Afganistan ya umurci gwamnan jihar yammacin Herat ,daya tura agajin kayayyaki na dala dubu 50.Duk da matsaloli da Afganistan din ke fuskanta na sake ginin kasar,gwamnati ta bayyana manufarta na taimakawa Iran da dan abunda Allah ya huwace mata a matsayin makwabciya.